Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama Mai Tsara Sakamakon Gasar Kwallon Kafa


Sakatare janar na 'yan sanda kasa da kasa kennan, Ronald Noble a lokacin da yake yi wa 'yan jarida magana akan shirya sakamakon gasa, a garin Kuala Lumpur, Malaysia, Fabrairu 21, 2013.

Hukumomin kasar Italiya sun ce sun kama wani mutum da ake kyautata zaton shine yake tsara yadda sakamakon gasar kwallon kafa zata kasance, bayan isarshi Milan daga Singapore.

‘Yan sanda a Cremona kasar Italiya, suna neman Admir Sujic, dangane da binciken da suke gudanarwa kan cogen sakamakon gasar kwallon kafar cin kofin kasashen turai da ya hada da wadansu gasar cin kofin duniya da kuma wasannin fidda gwani.

Tun farko rundunar ‘yan sandan kasa da kasa ta Interpol ta bayyana cewa, mutumin yana kan hanyarsa zuwa Singapore daga Italiya.

Hukumar ‘yan sandan tace ana kyautata zaton Sujic yana da alaka da Tan Seet Eng, mutumin da ake zargi da tsara cogen sakamakon wassaninin dake da cibiya a Singapore.

A wani taron kasa da kasa da aka gudanar kan cogen sakamakon gasa da aka gudanar a Maleshiya cikin wannan makon, babban magatakardan ‘yan sandan Interpol Ronald Noble ya yi gargadi da cewa, ba za a iya samun nasarar yaki da cogen sakamakon gas aba sai fa idan hukumomi suna samar da bayanai kan lokaci.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG