Accessibility links

'Yan Yawon Bude Idanu 19 Sun Mutu a Hadarin Jirgin Balon-Balo


Samfurin jirgin balom-balo da ya fashe ran Fabrairu 26, 2013.

Wani jirgin ‘yan yawo bude ido mai siffar balom-balo yayi hadari kusa da birnin Luxor a Masar, kuma ya kashe ‘yan yawon bude ido su 19 da suke ciki.

WASHINGTON, D.C - Mutane biyu ciki harda matukin jirgin sun tsallake rijiya da baya, bayanda jirgin ya kama da wuta san nan yayi bindiga lokacin yana shawagi kamar mita 300 a sararin samaniya, a yammacin gabar tekun Nilu.

Jami’ai suka ce mamatan sun hada da ‘yan kasar Faransa, Britaniya, da kuma wasu kasashe.

Wuri da jirgin yayi hadari shine tsohon babban birnin Masar mai tarihi, wurin yana ganin tururuwar ‘yan yawon bude ido wadanda suke zuwa domin ganin dadaddun wuraren ibada, fadan sarakuna da kushewa, da suka hada da inda aka binne wani basarake ko fir’aunan nan da ake kira Tutankhamun.

Tun a skerarar 1979 hukumar kula da al’adu da harkokin gargajiya ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO ta ayyana wurin a matsayin wuri mai dumbin tarihi a duniya.
XS
SM
MD
LG