Accessibility links

Tarzoma Ta Barke A Bangladesh


'Yan sandan kiyaye tarzoma a lokacin da suke yunkurin kwantar da rigima a garin Rajshahi, Bangladesh, Juma'a, Maris 1, 2013.

Akalla mutane 44 aka kashe a kazamin tashin hankalin da ya biyo bayan hukuncin kisan da wata kotu ta yanke wa wani mashahurin babban malamin Islama na kasar Bangladesh.

Rahottani sunce mace-macen baya-bayan nan sun faru ne a gundumar Gainbandha inda can ma aka share kwannaki biyu ana bata kashi tsakanin ‘yansanda da mutanen dake zanga-zangar nuna rashin amincewa da wannan hukunci.

Kuma ana sa ran cewa tashin hankalin zai ci gaba bayan sallar Jumu’ar yau. Aksarin wadanda aka kashe duk ‘yansanda ne suka bindige su jiya a gumurzun da aka yi tsakanin su ‘yansandan da masu zanga-zangar nuna jin takaici da hukuncin kisan da aka yanke wa Delwar Hossein Sayedee wanda akace an same shi da laifukkan da suka hada da fyade da kisan kai, duk a lokacin yakin da aka yi da Pakistan kan nemarwa Bangladesh ‘yancin kanta a shekarar 1971.

Kuma duk wannan tashe-tashen hankalin na jiya ya biyo ne bayan kiran da jam’iyyar shi Sayedeen ta Jamaat-e-Islami ta kira don a nuna jin haushi da hukuncin da aka yanke mishi.

Wani wakilin Muryar Amurka dake Dhaka yace wadanda aka kashen sun hada da ‘yansanda biyu, yayinda aka ji wa mutane sama da 200 rauni.
XS
SM
MD
LG