Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za'a Daure Sojojin Amurka A Japan


Okinawa, Japan

Wata kotun birnin Okinawa na kasar Japan ta yanke hukuncin daurin shekaru da dama akan wasu sojojin Amurka biyu da aka same su da laifin yi wa wata macce ‘yar Japan fyade da fashi da makami.

Wannan kotun ta gundumar Naha ta yanke hukuncin daurin shekaru 10 akan Christopher Browning akan laifin fyade da fashi da makami yayinda aka yanke hukuncin daurin shekaru 9 akan abokinsa Skyler Dozienwalker wanda shi kuma aka same shi da yi wa maccen fyaden taron-dangi.

Wadanan sojojin biyu, wanda aka tura can japan daga wurin aikinsu dake a tashar sojan jiragen ruwa dake a jihar Texas ta nan Amurka, ance sun yi wa matar fashi da fyaden ne a ran 18 ga watan Oktoban shekarar da ta gabata.

Duka mutanen biyu dai sun amsa laifukkan nasu. Wannan al’amarin ya janyo a saka wa dukkan sojojin Amurka dake Japan dokar ta-bacin hana musu fita.

Sai dai kuma duk da wannan dokar-ta-bacin, ana ci gaba da samun sojojin Amurka suna aikata laifukka barkattai a can japan, galibinsu a cikin mayen barasa.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG