Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutan Kenya Na Kada Kuri'a


Wata mata rike da danta na jefa kuri'a a kasar Kenya.

A Kenya al’umar kasar suna kada kuri’a a babban zabe kasa bayand a suka tsaya a layi na lokaci mai tsawo cikin lumana.

Zaben da ake gudanarwa yau litinin ya hada da zaben shugaban kasa, lamarin da shekaru biyar da suka wuce ya janyo tarzoma da ta halaka fiye da mutane dubu da dari daya.

Shugaban kasar mai barin gado Mwai Kibaki, da ‘yan takara da suke yakin a zabe su domin su maye gurbinsa duk sun yi kira da a gudanar da zabe cikin lumana.

‘Yan takara biyu da suke kan gaba a kuri’ar neman jin ra’ayin jama’a da aka gudanar gabannin zaben na yau watau Firayim Minista Raila Odinga da mukaddashin Firayim Minista Uhuru Kenyatta duk sun yi alkawarin zasu mutunta sakamakon zaben.

Hukumomi suka ce wasu hare-hare guda biyu da aka auna kan ‘yansanda a yau litinin a binrin Mombasa mai tashar jiragen ruwa da wani wuri kusa da birnin sun halaka akalla mutane 12.

Sun ce watakil wata kungiyar ‘yan aware ce ta kai hare haren, wadanda suka yi sannadiyyar mutuwar ‘yansanda bakwai.
XS
SM
MD
LG