Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Lokacin Shawarwari Da Iran Na Raguwa - inji Sakatare Kerry


Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry, a lokacin da yake tattaunawa da sakataren harkokin wajen Saudiyya a garin Riyadh, ran Maris 4, 2013. REUTERS/Jacquelyn Martin/Pool (SAUDI ARABIA - Tags: POLITICS) - RTR3EK39

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry yace lokacin da ya rage na ci gaba da shawarwari da Iran kan shirin Nukiliyarta bashi da tsawo.

Mr. Kerry ya furta haka ne yau litinin a Riyadh, bayan ya kammala shawarwari da ministan harkokin wajen Saudiyya Yerima Saud al-Faisal, wanda shi ma ya amince ba za’a dore da shawarwarin da Iran har abada ba”.

Haka ma a yau litinin Kerry yana ganawa da shugaba Mahmoud Abbas na yankin Falasdinu, mako biyu kamin ya rufawa shugaba Obama baya a ziyarar da zai kai Isra’ila.

Shawarwari da Mr. Kerry yake yi a Saudiyya yana daga cikin ajendarsa a ziyarar aiki ta farko da zai kai tun kama wannan aiki.

Ana sa ran zai kammala rangadin nasa da yada zango a hadaddiyar daular larabawa da Qatar.

Ahalinda ake ciki kuma shugaban hukumar hana yaduwar makaman kare dangi na Majalisar Dinkin Duniyam, Yukiya Amno yana kara matsin lamba kan Iran ta bada bayanai kan zargin ta na kera makaman Nukiliya, ya sake nannata kira ga Iran ta baiwa spetocin hukumar damar kai ziyara wasu muhimman sansanin sojin kasar.
XS
SM
MD
LG