Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Uhuru Kenyatta Na Kan Gaba A Zaben Kenya


Hotunan 'yan takarar shugaban kasa a Kenya.

Sakamakon farko na zaben da aka gudanar a kasar kasar Kenya na nuni da cewa, Uhuru Kenyatta yana kan gaba a zaben shugaban kasa.

WASHINGTON, D.C - Bayan kamala kirga kuri’in kimanin kashi arba’in bisa dari na mazabu yau Talata, Mr Kenyatta ya ba babban abokin hamayyarsa Raila Odinga rata tare da samun kashi 55 bisa dari na kuri’un yayinda Odinga yake da kashi 41 bisa dari.

Idan babu wani cikin ‘yan takarar da ya sami rinjaye a zaben za a je zagaye na biyu a watan Aprilu.

Mr. Kenyatta wanda shine mukaddashin Firai Ministan kasar Kenya, yana da gagarumin goyon baya a arewacin Nairobi babban birnin kasar, yayinda Mr Odinga yake kan gaba a kananan hukumin dake kudandin kasar.

Kimanin mutane miliyan 14 ne a kasar Kenya suka cancanci kada kuri’ar zaben shugaban kasa da na majalisa da sauran guraba. Mr. Odinga da Kenyatta sun yi alkawarin mutunta sakamakon zaben.

Mr. Kenyatta yana fuskantar tuhuma a kotun bin kadin manyan laifuka ta kasa da kasa bisa zargin cewa, ya kitsa rikicin kabilancin da ya biyo bayan zaben shugaban kasa da aka gudanar a shekara ta dubu biyu da bakwai.

Sama da mutane dubu daya da dari daya aka kashe a wannan tashin hankalin.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG