Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

China Ta Amince Da Amurka Wajen Ladabtar da Koriya Ta Arewa


Jami'an gwamnatin China.

Jami’an diplomasiyar Majalisar Dinkin Duniya sun ce Amurka da China sun cimma matsaya kan sababbin takunkumin ladabtar da Koriya ta Arewa sabili da kwajin makami mai linzamai na baya bayan nan da tayi, yayinda Pyongyang take barazanar watsi da yarjejeniyar da ta shafi manyan makamai da ta kawo karshen yaki da Koriya ta arewa da aka yi tsakanin shekara ta dubu da dari tara da hamsin zuwa da hamsin da uku.

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya yi wani zaman bayan fage kan Koriya ta Arewa yau Talata, jami’an diplomasiya kuma suka shaidawa manema labarai cewa, suna kyautata zaton za a kada kuri’ar amincewa da kudurin a karshen makon nan. Ba a bayyana cikakken bayani kan daftarin ba tukuna.

Kwamitin sulhun da murya daya, ya kushewa gwajin makamin da Koriya ta arewa tayi ranar 12 ga watan Fabrairu da cewa, ya sabawa takunkumin da Majalisar Dinkin Duniya ta kakabawa ayyukan nukiliya na Koriya ta arewa. Pyongyang tace gwajin da tayi na uku wanda kuma shine yafi duka karfi, tayi ne sabili da Amurka babban abokiyar gabarta.

A halin da ake ciki kuma, yau talata Koriya ta Arewa ta kara zafafa kurinta tare da bayyana cewa zata soke yarjejeniyar ta aka cimma a shekara ta dubu da dari tara da hamsin da uku muddar Seoul ta ci gaba da shirinta na gudanar da atisayen da ta sabawa yi shekara shekara na hadin guiwa da Amurka. Babban kwamandan rundunar sojojin Amurka ya yi gargadin kai wani salon hari da nufin hada kan yankin Koriyan da ake fama da rarrabuwar kawuna.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG