Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Cigaba Da Kirga Kuri'u A Kenya


Mazauna wata unguwa na kallon kirgen sakamakon zaben shugaban kasa a Kenya ran Maris 5, 2013.

To har yanzu dai jami’an hukumar zabe ta Kenya na cigaba da kirga kuri’un zaben shugaban kasa da kenyawa suka jefa ran Litinin, kuma har yanzu dai, Uhuru Kenyatta ne akan gaba.

WASHINGTON, D.C - Kuri’un da aka kirga basu fi rabi ba, kuma sun nuna Mr. Kenyatta a gaba da kaso 53 cikin dari, yayinda abokin takararsa Firai Minista Raila Odinga yake bin shi da kaso 42 cikin dari.

Jami’an hukumar zabe sunce an yi watsi da kuri’u sama da dubu dari 3 da 30 wadanda suka saba dokokin zabe. Manazarta na bada hasashen da yace ba lallai bane Mr. Kenyatta ya samu sama da kuri’u 50 da ake bukata domin lashe zaben, kuma idan hakan ya faru, to dole sai an kara jefa zaben raba gardama a watan Afrilu.

Masu sa ido daga kasashen waje sunce an gudanar da zaben a cikin kwanciyar hankali.

John Stremlau na cibiyar Carter dake nan Amurka, wanda kuma yaje can Kenya din domin ganin yadda aka gudanar da zaben, yace tawagarshi zata wallafa rahoto yau laraba, kuma John din ya yaba wa hukumar zaben Kenya akan abun da ya kira zabe mai cike da “kwanciyar hankali” da kuma “walwala”.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG