Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Dakatar Da Kidayar Kuri'ar Kenya - inji Raila Odinga


Manyan 'yan takarar shugabancin kasar Kenya.

Dan takaran mataimakin shugaban kasa ga Raila Odinga dake takaran shugaban kasa a zaben kasar Kenya, yace yadda ake gudanarda kidayar kuri’un da aka jefa a zaben ba ya bisa kan hanya, saboda haka ya kamata a tsaida kirgar.

WASHINGTON, D.C - A yau Alhamis ne Kalonzo Musyoka yake magana da manema labarai a birnin Nairobi, a daidai lokacinda ake ci gaba da kirga kuri’un da hannu bayanda na’urorin komputa da ake amfani da su, suka ja suka tsaya.

I zuwa safiyar yau Alhamis dai an kirga kuri’u kusan rabin milyan kuma sakamakon na nuna cewa Uhuru Kenyatta na da kashi 53% na kuri’un yayinda abokin takarar nashi Raila Odinga ke da kashi 42%.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG