Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yanke Wa Silvio Berlusconi Hukuncin Dauri A Gidan Kaso


Tsohon Firai Ministan Italia, Silvio Berlusconi

Wata kotun kasar Iyaliya ta yanke hukuncin daurin shekara daya a kurkuku akan tsohon frayim-ministan kasar Silvio Berlusconi¸wanda daya ne daga cikin manyan attajiran kasar da suka mallaki kafofin watsa labarai.

WASHINGTON, D.C - An same shi ne da laifin tona asirin wasu bayanan asiri da ‘yansanda suka dauka.

A yau Alhamis ne kotun ta yanke wannan hukuncin wanda Mr. Berlusconi na da ‘yancin ya daukaka karar zuwa gaba in bai gamsu da it aba, kuma wannan daukakar zata sa a dakatar da aiwatar da hukuncin.

Bayanin asirin da akace tsohon frayim-ministan din ya bayyana yana da alaka ne wani binciken asiri da hukumomin ‘yan sanda suka gudanar dangane da yunkurin wasu na kwace wani banki.

Ko bayan wannan hukuncin, tsohon frayim-ministan na jiran wasu shara’oi biyu da za’a yi mishi a cikin wannan watan: daya kan kin biyan haraji, ta biyun kuma kan zinar da yayi da wata karuwa da aka ce bata balaha ba.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG