Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Bafaranshen Da Ake Garkuwa Da Shi A Mali


Kamfanin dillancin labaran kasar Mauritania da ake kira ANI a takaice ya ce al-Qaidar arewacin Afirka ta kashe Philippe Verdon

Kamfanin dillancin labaran kasar Mauritania ya ce al-Qaida ta kashe dan kasar Faransar da ta ke yin garkuwa da shi a kasar Mali

Kamfanin dillancin labaran wata kasar Afirka ya ce a wani matakin ramuwar gudunmowar sojojin da Faransa ta kai kasar Mali, Al-Qaidar kasashen arewacin Afirka ta kashe wani dan kasar ta Faransa wanda ta ke yin garkuwa da shi.

Kamfanin dillancin labaran kasar Mauritania, ANI, ya fada a jiya talata cewa ta wayar talho aka sanar da shi cewa an kashe Philippe Verdon wanda ake yin garkuwa da shi.

Kamfanin dillancin labaran ya ruwaito wani kakakin al-Qaida a kasashen Musulmin Arewacin Afirka, ya na cewa ranar 10 ga watan maris aka kashe shi.

Ba a tabbatar da labarin kisan ba, kuma ma’aikatar harakokin wajen kasar Faransa ta ki cewa uffan da aka tuntube ta da yammacin jiya talata.

Philippe Verdon shi ne daya Bafaranshen da aka sace tare da wani a cikin watan nuwamban shekarar 2011 a garin Hombori da ke arewacin kasar Mali. An bada labarin cewa wani balaguron kasuwanci ne a ya kai shi yankin.
XS
SM
MD
LG