Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane 27 Suka Rayu A Hadarin Jirgin Kwale-Kwale


Masu agajin gaggawa kennan a lokacin da suke neman mutane da suka rayu a hadarin jirgin ruwa.

Hukumomin Nigeria sunce mutane akalla 27 aka ceto da ransu daga cikin wani jirgin kwale-kwalen da ya kife cikin makon jiya a kudancin kasar.

WASHINGTON, D.C - Ance mutanen dake cikin jirgin sun fi 130 amma izuwa yanzu gawwakin mutane 9 kawai aka tsamo.

Hukumomin na Nigeria sunce har yanzu suna ci gaba da nema da fatar gano karin mutane da ransu daga cikin wadanda ke cikin wannan jirgin ruwan da tun Jumu’ar da ta gabata ya nutse a wani wurin da tazarar km 60 ta raba shi da birnin Calabar dake jihar Rivers.

Wani ma’aikacin bada agajin gaggawa Vincent Aquah yace biyu daga cikin mutanen da suka tsira da ransu sun tsria ne saboda sun kama wani butuntun iskar gas, suka rike shi gam.

Daya daga cikin mutanen biyu, wani dan kasar Togo da ake kira Kieve Sani yace jirgin nasu ya soma nutsewa ne bayanda injin dinsa ya mutu.

Ance da yawa daga cikin wadanda abin ya shafa ‘yan ci rani ne dake kan hayarsu ta zuwa Gabon wajen neman aikin yi.
XS
SM
MD
LG