Har zuwa yanzu dai ba wata kungiyar da ta dauki alhakin kai harin, amma dai an san cewa wannan shine harin farko da aka kai a can Timbuktu tun lokacinda sojan kasa-da-kasa a karkashin Faransa suka fara yunkurin koran mayakan ‘yan kishin Islaman da suka mamaye sashen arewancin Mali din.
A jiyan ne kuma shugaban kasar Faransa din Francois Hollande yake cewa ana cikin kashin karshe na kamalla aikin da sojan Faransa suka je yi a can Mali.
Sai dai wasu na jin tsoron muddin faransa ta janye sojojinta 4,000 dake Mali, mayakan ‘yan kishin Islama masu daurin gindin al-Qaida zasu sake dawowa nan arewancin Malin.