Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Afirka Ta Kudu Ta Ce An Kashe Sojojinta 13 A Bangui


Kwambar motocin sojojin Chadi wadanda suka shiga cikin jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a watan Janairu don dafa wa gwamnati.

Shugaba Jacvob Zuma yace wasu sojojin na Afirka ta Kudu su 27 sun ji rauni, yayin da guda daya ya bace.

Afirka ta Kudu ta ce an kashe mata sojoji 13, wasu 27 kuma suka ji rauni, a fadan da suka gwabza da ‘yan tawaye a babban birnin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Shugaba Jacob Zuma yace har yanzu ba a san inda wani sojan guda daya yake ba a bayan wannan fadan da aka fara shi ranar asabar a birnin Bangui.

Gamayyar ‘yan tawayen Seleka ta kwace birnin jiya lahadi, abinda ya tilasta ma shugaba Francois Bozize arcewa.

Mr. Zuma yace Afirka ta Kudu tana adawa da duk wani yunkurin kwace ikon mulki da karfi, kuma mutuwar wadannan sojoji ba zata hana kasar kokarin hana kifar da gwamnatocin da aka zaba ta ba.

Afrirka ta Kudu ta tura sojoji 200 domin tallafawa rundunar sojojin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon, yayi Allah wadarai da abinda ya kira kwace mulki ta hanyar da ta saba da tsarin mulki wanda ‘yan tawayen suka yi, yana mai kiran da a gaggauta maido da yin aiki da tsarin mulkin kasa.

A yau litinin kuma, Kungiyar Tarayyar Kasashen Afirka ta dakatar da wakilcin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a cikin tarayyar, ta kuma bayar da umurnin kafa takunkumi a kan shugabannin ‘yan tawayen saboda kwatar mulkin da suka yi.

Har yanzu ba a bayyanawa duniya inda shugaba Bozize yake ba. Wasu rahotanni sun ce ya tsallaka kogin dake iyaka da babban birnin ya shiga kasar Kwango ta Kinshasa, amma jami’an Kwango sun ce ba ya cikin kasarsu.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG