Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bosco Ntaganda Ya Bayyana A Gaban Kotun ICC


Congolese warlord Bosco Ntaganda looks on during his first appearance before judges at the International Criminal Court in the Hague, March 26, 2013.

Tsohon janar na sojan Congo da ya juye ya koma madugun ‘yantawaye, Bosco Ntaganda yayi bayyanarsa ta farko a gaban alkallan Kotun Laifukka ta Duniya (ICC) a yau Talata, fiyeda shekaru bakwai bayanda kotun ta bada samamcin a je a kamo mata shi.

WASHINGTON, D.C - Ana tuhumar Ntaganda da laifukkan yaki guda bakwai da kuma laifukka ukku na gallazawa Bil Adama.

Lauyoyin kotun ta ICC sun ce a matsayinsa na kwamandan mayakan ‘yantawayen Junhuriyar Demokradiyar Congo, shine yake da alhakin cusa yara kanana cikin yakin bada son ransu ba da kashe-kashen gilla da fyaden da aka yi wa mata da yawa.

Manufar wannan zaman Kotun na yau dai shine don a bayyanawa Ntaganda laifukkan da ake tuhumarsa da aikatawa da kuma a tsaida ranar da za’a soma ainihin ita shara’ar tashi.

A cikin makon jiya ne dai Ntaganda ya kai kansa opishin jakadancin Amurka dake Rwanda, ya nemi a aika shi zuwa kotun ta ICC dake Hague.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG