Accessibility links

Jami’an tsaro a kasar Kenya sunce a kalla mutane 7 ne suka mutu bayan wani hari da wani gungu ya kaiwa wani gidan caca a garin Malindi dake bakin gabar teku, kuma gungun yayi arangama da ‘yan sanda.

WASHINGTON, D.C - Jami’ai sunce ‘yan sanda sun harbe, kuma sun kashe maharan su 6, wadanda suka kaiwa Malindi Casino hari a safiyar yau alhamis. Dan sanda guda daya ya rasa ransa a wannan arangama.

Shugaban ‘yan sanda na wannan lardi, Aggrey Adoli yace jami’ai sun kama maharan guda 4, kuma suna cigaba da neman ragowa.

Ana kyautata zaton maharan, ‘yan kungiyar wariya ce ta Mombasa Republican Council, wadda aka dora wa alhakin hare-hare a baya.
XS
SM
MD
LG