Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Sudan Ta Saki 'Yan Adawa Su 7


Fursinonin Siyasa Sudan kennan a lokacin da aka sake su daga Kober Prison a birnin Khartoum, Afrilu 2, 2013.

Jami’ai a Sudan sun saki fursinonin siyasa su 7, kwana daya bayan da Shugban Sudan Omar al-Bashir ya bada umarnin a saki duka ‘yan zaman kason.

WASHINGTON, D.C - Mazan su shida, da mace daya, za’a sake su yau Talata daga gidan yarin Kober dake birnin Khartoum.

Dukanninsu mambobin kungiyar adawar kasar ne.

Ana tsare da su tun watan Junairu, bayan da suka sa hannu akan wata takarda a kasar Uganda, takardar tana kiran da a tumbuke Shugaba Bashir.

An bude taron majalisar dokoki ta kasa jiya litinin, inda Mr. Bashir ya bada umarnin sakin duka ‘yan siyasan, a wani yunkuri na kokarin hada tattanawa da kungiyoyin tawaye da adawa akan sabon kundun tsarin mulkin kasar.

Ana kyautata zaton gwamnatin Sudan na tsare da daruruwan mutane wadanda sukayi zanga-zanga, ko suka nuna adawarsu a fili.

Gwamnatin tayi ta yakar ‘yan tawaye a Darfur tun shekara ta 2003, da kuma wasu ‘yan tawayen a jihohi biyu dake kudancin kasar tun shekara ta 2011.

I yanzu dai, ba’a tabbatar da lokacinda za’a saki sauran mutanen dake tsare ba.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG