Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Magoya Bayan Henrique Caprilles Zasu Yi Zanga-zanga A Venezuela


Supporters of opposition leader Henrique Capriles face off against riot police as they demonstrated for a recount of the votes in Sunday's election, in Caracas, April 15, 2013. Hundreds of protesters clashed with police in the Venezuelan capital on Monday

Magoya bayan dan takaran shugaban kasan Venezuela da aka kada, Henrique Capriles sun ce suna shirin gudanarda gagarumar zanga-zanga a rana ta biyu don nuna cewa basu yarda da kayen da aka ce an yi wa maigidan nasu a zaben shugaban kasan da aka kamalla a cikin wannan makon ba.

WASHINGTON, D.C - A irin wannan zanga-zangar da suka gudanar a jiya a birnin Caracas, magoya bayan Mr. Capriles sun bi tituna suna ta buga kwannukan girki da kona shara a lokacinda suke neman lalle a sake kirga kuri’un da aka jefa a zaben.

‘Yansanda sun kalubalance su, har suka jefa musu barkonon tsohuwa don tarwatsa taron.

Ko bayan birnin na Caracas ance an gudanarda irin wannan zangazanga ta ‘yan adawa a wasu lardunan kasar.

An soma wannan rigingimmun ne jim kadan bayanda Hukumar zaben Veneuela ta tabattarda cewa Nicolas Maduro ne ya lashe wannan zaben da aka yi a ranar lahadin shekaranjiya.

Mr. Maduro, wanda marigayi tsohon shugaban venezulea Hugo Chavez da kansa ya zabo ya tsaida shi, ya lasher zaben da kuri’u kalilan ne: ya sami 50.7% yayinda Mr. Capriles ya tashi da 49.1%.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG