Gwamnatin Chadi ta ce wannan gungu na "mutane 'yan kalilan" sun shafe watanni fiye da hudu su na kitsa yadda "zasu gurgunta cibiyoyin gwamnatin jamhuriya."
A cikin wata sanarwar da aka bayar vyau laraba, wani kakakin gwamnatin Chadi ya ce sojojin kasar sun "birkita" masu kulla makarkashiyar, suka kama su suka mika su hannun masu gabatar da kararraki gaban kotu.
Sanarwar ba ta bayyana mutanen da aka kama din ba, amma majiyoyin tsaro sun ce sun hada da fararen hula da sojoji, da kuma wani sanannen dan hamayya mai suna Saleh Maki.
Kasar Chadi ta sha fama da juye-juyen mulki da tawaye, ciki har da juyin mulkin da shi kansa shugaban kasar na yanzu Idris Deby yayi a shekarar 1990.