A cikin kudin da aka ware ma jihohi tara a kashin farko, jihar Bauchi zata samu nera miliyan dubu daya da miliyan dari bakwai. To sai dai babu wanda kason suka shigo hannunsa tukunna a jihar Bauchi. Wani Alhaji Auwalu Karfen Ningi ya ce shi da sauran mutane talatin da hudu da suka yi asarar dukiyoyinsu ko kwabo basu samu ba tukunna. Sun tattaka zuwa ofisoshin karamar hukuma da na jiha basu ci nasara ba. A jihar jami'an gwamnati sun ce su ma a kafar radiyo suka ji amma babu abun da ya shigo aljihun gwamnatin jihar game da biyan diyar.
Wakilinmu Abdulwahab Mohammed ya yi karin bayani a rahotonsa.