Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Scolari Yace Ya San Abinda Ya Hana Neymar Taka Rawa A FC Barcelona - 3/4/2014


Neymar
Neymar
Kwach na kasar Brazil, Luiz Felipe Scolari, yace ya san dalilin da ya sa Neymar ba ya taka rawa yadda aka yi tsammani a kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, amma kuma yace dan wasan zai iya zamowa daya daga cikin manyan taurari na gasar cin kofin duniya da za a yi nan da watanni a Brazil.

Kafofin labarai na kasar Spain sun yi caa a kan Neymar mai shekaru 22 da haihuwa, tun lokacin da Barcelona ta kashe kudi mai dan karen yawa wajen sayensa, amma kuma ba ya takawa yadda aka zata.

Scolari yace dalili shi ne, tsarin kwallon Barcelona yayi dabam da wanda Neymar ya saba da shi a Santos kafin ya koma. Yace a Barcelona, an maida Neymar ya koma bugawa daga gefen dama, yayin da a can baya ya saba da buga kwallo daga inda yake da fili sosai a gabansa.

Kwach din na Brazil yace Neymar yana da matukar muhimmanci ga kungiyar kwallon kafa ta kasar Brazil, kuma yana iya zamowa daya daga cikin zakarun gasar cin kofuin duniya ta bana. Watakila ma, yace Neymar zai shana fiye da kowane dan wasa a lokacin gasar.
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:10 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG