Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji Sun Kona Motocin Sufuri na Jihar Lagos


Sojoji

Sojoji a Lagos , sun kona motocin sufuri hudu sun kuma lalata hudu malakan Gwamnatin jihar Lagos.

Wannan ya biyo bayan banke wani soja da daya daga cikin motoci tayi akan babban titin Ikorodu a garin Lagos.

Kamar yanda wadanda suka gani da idanusu suka sheda wa muryar Amurka , suce daya daga cikin bas-bas din ne ya saki hannun sa ya banke sojan wanda ya mutu nan take.

Wani da muryar Amurka ta ji ta bakinsa yace wannan abun da sojojin suka yi bai dace ba, idan laifi aka yi masu su kai gaban hukuma ko kuma kotu amma bawai su dauki doka a hannun sub a.

Amma a wani lokaci can baya Gwamnan Lagos Babatunde Raji Fashola, yasa an kama wani soja ma mukamin kanal saboda ya bi hanyar da aka yi na masamman domin motocin sufurin jihar Lagos, wannan ma ana iya cewa yasa sojojin daukan wannan matakin.

Domin wannan lokacin gani su keyi kamar wani tozartawa ce aka yiwa daya daga cikin shugabaninsu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:39 0:00
Shiga Kai Tsaye

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:39 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG