WASHINGTON, DC —
A yau dandalinvoa, yayi nazari ne akan yanda Gwamnatin jihar kano, ke gudanar da aikin ciyarwa na abincin azumi.
Mai kula da shirin dangane da yanda yake dahuwa da kuma rabon abinci yace akwai cibiyoyi dari da saba’in da shida.
Abana yace an kashe fiye da Naira Miliyan dari biyu da hamsin domin ciyar da mutane a wannan wata mai alfarma.
Yace bana an fara tsarin da wuri, yana mai cewa bara an da cibiyoyi dari da ashirin da ashirin amma bana kuwa ya karu zuwa dari da saba’in da shida.