Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Brazil ta Sha kashi a Hannun Jamusawa


Jamus da Brazil

To fa jama’ar kasar Jamus sun farka wayewar gari suka tarar kungiyar kwallon kafarsu ta ragargaza Brazil da ciya-ciyayy 7-1 a wasan kusa da karshe a gasar cin kofin duniya, lamarin da yazo musu ba ma kamar mafarki bane, amma matsayin wani abu da dakyar suka yarda dashi.

Jaridar da tafi kasuwa a can Jamus din ita kanta rubutawa tayi a shafin farko “7-1, babu abun cewa”.

Jaridar tayi amfani da shafuka 6 inda ta wallafa hotunan ‘yan was anta suna cin kwallaye, kuma suna murna da farin ciki, sannan ta yabawa Mira Klose, inda ta kira shi shahararren dan wasan kwallon kafa.

Jaridar ta cigaba da yabon kungiyar inda tace, baza a taba mantawa da ita ba a tarihin kwallon kafar Jamus, ta kuma kara da cewa ci 7 da 1 kamar daukar kofin ne baki dayansa.

Ko shahararren tsohon dan wasan Jamus wanda ya ci kofi a matsayinsa na dan wasa, da kuma kwach, cewa yayi “Mene ne ya faru? Da kyar hankali ka dauki wannan lamari”.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:00 0:00
Shiga Kai Tsaye

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG