Wasu 'yan bindigar da ba a tantance ko su wanene ba, sun kai farmaki daren jiya a garin Soro, inda suka kashe Hakimin kasar Soro, Alhaji Abdul-Rahman Isa Baba, tare da wasu mutanen.
Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sanda a Jihar Bauchi, DSP Haruna Mohammed, yace a bayan hakimin na Soro, akwai wasu 'yan kasuwa guda biyu da 'yan bindigar suka kashe.
Yace 'yan bindiga su 6 ne suka kai wannan farmakin a kasuwar garin Soro, kuma ana kyautata zaton cewa 'yan fashi ne. Kasuwar ta garin Soro tana ci kowace ranar asabar.
DSP Mohammed yace su na ci gaba da binciken wannan harin da aka kai da misalin karfe 7:45 na daren asabar.
Idan ba a mance ba, kwanakin baya ne wasu 'yan bindigar da wasu suka alakanta su da kungiyar Boko Haram suka sace wani dan kasuwa a garin na Soro, Alhaji Manu Soro, wanda daga bisani aka sako a bayan da a bisa dukkan alamu aka biya kudin fansarsa.
Haka kuma, an yi imanin cewa 'yan Boko haram din sun kafa sansanonin horas da mayakansu cikin dazuzzukan dake yankin garin na Soro, mai iyaka da Darazo, inda a watan da ya shige sojoji suka tarwatsa wani sansanin na 'yan Boko Haram a dajin Balmo.