Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin British Airways Ya Dakatar Da Zuwa Wasu Kasashen Don Fargabar Ebola


Kamfanin safarar jiragen sama babba na biyu ya dakatar da zuwa wasu kasashen Afirka ta Yamma a saboda barkewar annobar cutar Ebola a yankin.

A yau talata kamfanin safarar jiragen saman British Airways yace ya dakatar da sauka ko tashi daga kasashen Liberiya da Saliyo a saboda tabarbarewar ayyukan lafiya a kasashen biyu. Yace wannan dakatarwa zata yi aiki har zuwa ranar 31 ga watan Agusta.

A ranar 2 ga wata, kamfanin safarar jiragen saman Emirates na Dubai ya dakatar da sauka ko tashi a kasar guinea.

Wadannan kasashe 3 sune suka fi fama da annobar cutar Ebola wadda ya zuwa yanzu ta kashe mutane kusan 900 a wannan yankin.

XS
SM
MD
LG