Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rikicin Siyasa a Taraba, 'Yansanda Sun Tarwatsa 'Yan Banga


Jihar Taraba, mukaddashin Gwamnan jihar Taraba, Sani Danladi.

Sakamakon fidda dan takara a Abuja, magoya bayan wasu 'yan takara sun fusata.

Rundunan yan sandan jihar Taraba ta samu nasarar tarwatsa wasu gungun yan bangan siyasa da suka tada ya mutsi a garin Jalingo,fadar jihar.

Wannan hargitsin dai ya biyo bayan matakin da kwamitin zartaswa na jam’iyar PDP ta kasa ta dauka, na baiwa Mr Ishaku Darious kujerar takarar gwamnan jihar,matakin da wakilan zabe na jam’iyar da aka zaba, wato delegates suka ce,ba zata sabu ba,don haka suka garzaya kotu suna kalubalantar matakin.

Al'amarin yasa magoya bayan bangarorin da basu amince da zaben ba, suka hau kan tituna suna yaga hotunan yakin neman zabe na banagaren da suka sami nasara.

Ga karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:51 0:00

XS
SM
MD
LG