Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Tsaro Sun Bukaci Jama'a Su Koma Garuruwansu Da Aka Kwato Daga Hanun 'Yan Boko Harama.


Fadar Mai Martaba Sarkin Mubi Bayan Da Sojojin Gwamnati Suka Shiga Garin, 30 Nuwamba, 2014

Hakan ya biyo bayan sake kwato Gombi da Hong da Mubi daga hanun 'yan binidgar.

Shugabanin Hukumomin tsaro a jihar Adamawa,sun ziyarci yankunan da aka kwato daga hannun yan Boko Haram, inda suka gamsu da matakan da aka dauka,wanda adon haka suka bukaci al’ummomin yankunan da aka kwato wato Gombi,Hong,Maiha da kuma Mubi das u komo babu matsala.

Jami’an tsaron wanda suka komar da mai martaba Sarkin Mubi,Alh.Abubakar Isa Ahmadu zuwa fadarsa day an boko haram suka kwace,sun tabbatar da kare rayuka da kuma dukiyar jama’a.

Wannan dai na zuwa ne, yayin da ake cigaba da fatattakar mayakan na Boko Haram,wanda kawo yanzu har an kwato wasu garuruwa a yankin Michika,wanda shima ya fada hannun mayakan na Boko Haram.

Ga karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00

XS
SM
MD
LG