Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jawabin Janar Buhari da Gwamna Wamako Akan Dage Zabe


Janar Mohammadu Buhari mai ritaya, ya fadi cewa wannan hurumin hukumar zabe ne ta dage zabe in da bukatar yin haka ba ra'ayin wani ba.

Da yake jawabi a taron gangamin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a birnin Sokoto, gwamna Aliyu Magatakarda Wamako yayi kakkausar suka akan kalaman da mai ba shugaban kasa shawara akan sha’anin tsaro yayi, na bukatar dage gudanar da babban zaben watan gobe. Abinda gwamnan ya bayyana a zaman wani yinkuri na kawo cikas a tsarin zaben.

Dalilin wannan kiran da mai ba shugaba shawara yiyi shine ganin cewa har yanzu ba a gama rarraba katun did-din-din na zabe ba kuma zaben na karatowa.

Haka shi ma dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC Janar Mohammadu Buhari mai ritaya, ya fadi cewa wannan hurumin hukumar zabe ne ta dage zaben in da bukatar yin haka ba ra'ayin wani ba.

Da alama dai cincirundon taron jama’a a gangamin yakin neman zabe a jihohiin sokoto, Kebbi da Zamfra da aka yi ya gamsar da Janar Buhari, wanda ya bayyana cewa da alamun nasara amma yana ganin akwai sauran aiki a gaba.

Shi ma shugaban jam’iyyar APC ta kasa chief John Oyegun, ya nuna mamakinsa ganin yadda ya ga taron jama’ar na neman canji a kasar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00
Shiga Kai Tsaye

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG