Matasa a Najeriya na ganin cewar rashin zaben shuwagabani adilai masu tausayin talakawa ne ke kawo rashin zaman lafia a kasar. Don haka suna ganin lokaci yayi, matasa su farga kada ku bari ayi amfani daku wajen cinma wani buri na son kai, sun kuma yi kira dacewar matasa kada su bari ayi amfani da kudi wajen juyamusu ra’ayinsu don zaben dantakara wanda ba nagari ba.
Wadannan matasan dai naganin cewar hukumar zabe me zaman kanta wato INEC, da jami’an tsaro suke da hakin kai sakamakon zaben shelkwata tun daga matakin gunduma har zuwa tarayya, don haka suna kira garesu da su yi kokarin yin adalci kada su chanza sakamakon zabe kafin isa wajen bayyanar da shi.
Sun yi nuni da cewar idan suka chanza wannan sakamakon zaben to lallai shine zai kai ga rashin kwanciyar hankali a kasar baki daya. Sun kuma yi shiri don ganin ba’a chanza sakamakon zabe ba daga matakin local gwament har zuwa jiha da kuma tarayya, wannan matakin nasu ba zai samu nasara ba har sai sun samu goyon bayan ‘yan siyasa da jami’an tsaro dama duk wasu masu hannu da ruwa a harkar zabe, kuma suna kara kira ga al’umah da suyi zabe cikin kwanciyar hankali da lumana, kana subi doka da oda a kowane hali.