Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Bindiga Ya Kashe Mutane 2 A Denmark


Frayin ministan Denmark Helle Thorning-Schmidt, lokacinda ta kai ziyara inda aka kai harin.

An auna harin ne kan wani mai zane da yayi batunci kan Manzon Allah.

A Denmark, 'Yansandan kasar suka ce wani mutum da aka harbe a harabar wurin ibadar yahudawa a birnin Cpoenhagen ya mutu, a hari na biyu da aka kai a babban birnin kasar Jiya Asabar.
Wannan harin an kai shi ne sa'o'i bayan da wani dan bingidga daya dauke da makami mai sarrafa kansa ya bude wuta a wani taron da ake yi gameda 'yancin magana a wani wurin cin abinci a birnin Copenhagen, ya kashe mutum daya, ya raunata 'yansanda uku.

PM kasar Helle Thorning Schmidt, ta kira harbin a zaman "harin ta'adanci". Shaidu suka ce sunji harbe harbe sau da dama, kamin maharin ya tsere cikin wata bakar mota. Daga bisani 'Yansanda suka gano motar. Amma suna ci gaba da neman su.

Daga nan 'Yansanda suka gargadi mutane su kula sosai, kuma su bi umarnin jami'an tsaro su zauna cikin gidajensu. Babu bayanai nan da nan kan ko akwai nasaba tsakanin hare haren biyu.

Mutumin da ake zargin aka auna da harin da aka kai na farkon, shine mai zanen nan, dan kasar Sweden mai suna Lars Vilks, wanda yayi kaurin suna wajen zane-zane, wadanda suke janyo cece kuce, ciki harda zanen da yayi gameda manzon Allah a 2007, wanda yayi matukar harzuka musulmi, tun can ake ta yi masa barazana Vilks dan shekaru 68 da haifuwa barazana.

Amurka tayi Allah wadai da harin da aka kai a binrin na Copenhagen, inda ta kira harin abun bakin ciki.

Dan zanen Vilks ya tsalake rijiya da baya, haka shima jakadan Faransa a a Denmark Francois Zimmery wanda yake halartar taron. An shirya jakadan na Faransa zai yi magana kan yadda harin da aka kai kan ofishin mujallar barkwanci da ake kira Charlie Hebdo da kuma kantin yahudawa a birnin Paris cikin watan jiya.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG