Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bukola Saraki Ya Zama Shugaban Majalisar Dattijai


Ginin majalisun tarayyar Najeriya

A wani matakin hadin kai a tsakanin 'yan APC magoyta bayan Bukola Saraki da kuma 'yan jam'iyyar adawa ta PDP, an zabi tsohon gwamnan na Jihar KWara a zaman shugaban majalisar dattijai.

A wani matakin da yayi kama da abubuwan da suka faru a majalisar wakilan Najeriya a 2011, 'yan jam'iyyar APC masu goyon bayan Bukola Saraki sun hada kai da 'yan jam'iyyar adawa ta PDP suka zabi tsohon gwamnan na jihar Kwara a zaman sabon shugaban majalisar dattijai.

Haka kuma, an zabi dan jam'iyyar PDP mai adawa, Ike Ekweremadu, a matsayin mataimakin shugaban majalisar, ya kayar da sanata Ali Ndume na jam'iyyar APC a wannan zaben da mafi yawan 'ya'yan jam'iyyar APC ba su cikin zauren a lokacin da aka gudanar da shi.

Sanatoci 57 kawai suka halarci zaben shugabannin, yayi9n da wasu sanatoci 51, akasarinsu 'ya'yan jam'iyyar APOC, suke can dakin taro na kasa da kasa inda suka ce an tura su domin ganawa da shugaba Muhammadu Buhari.

Wakiliyarmu Madina Dauda, ta ce yanzu haka dai ana can ana kokarin yin zabe a majalisar wakilai.

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG