A duniyar finafinai kuwa yau mun samu zantawa da jarimar nan ta duniyar Hausa fim, Maryam Sulaiman wace akafi sani da Maryam CTV. Wadda take a da ma’aikaciyar gidan CTV ce amma daga bisani sai ta koma harkar fim. Tace dai tafara wanna harakar fim inne don ganin cewar wanna wata damace da zata iya amfani da ita don wayar da kan al’uma. Domin kuwa ta harkar fim akansamu mutane da dama da suke daukar wasu darussa, don haka take ganin yakamata ta shiga don bada tata gudunmawar.
Ta bayyanar da cewar, bangaren da ake bata tana fitowa na uwa kuma mai hakuri, wanna bangaren nabata sha’awa domin kuwa tanason yadda take fitowa a matsayin uwa don azahirance ita uwace, don haka wanna bangaren yana burgeta matuka. Kuma kada mutane su daukacewar tafison wannan bangaren ne don tanaso tanuna haka take a zahirance, domin kuwa su wadanda ake bama wasu bangaren sai suce me?
Ta kara dacewar, ai jama’a sune mutane don haka tanajin dadin yadda take samun masu sonta a cikin al’uma, wani abu dai wanda kan sosa mata rai a wasu lokutta da mutane shine, yadda a wasu lokutta mutane sukan hanasu gudanar da wasu abubuwan walwala garesu, domin kuwa idan suna tafiya mutane kansamusu ido fiye da kima.
A kuma irin kalubale da take fuskanta, ba wani abu bane illa yadda a lokaci da dama sukanzo wajen gabatar da wani fim amma basu samun gabatarwa sai har lokaci ya kure basu yi komai ba, to azahirin gaskiya jira shine abu da bataso ko kadan, tafiso ace kowane rana idan baza’a nuna gidan kuba, to kada kuzo sai ranar da kawai za’a nuna gidan mutu ne sai su zo, ta haka za’a gujema irin wanna bata lokacin ga jama’a. Tana kumaburin Allah, ya nuna mata ranar da zata zama mai rubutawa da bada umurni na fim in kanta don tabar tarihi a rayuwa.