Idan har zan saka kafata a cikin dakin da zan gana, da masu daukar aiki, don ganawa aga ko na can-can-ci wannan matsayin ko aiki, ba shakka zan samu aikin.
Masu neman aiki ku sani fa, duk lokacin da zaku nemi aikin gwamnati ko ma’aikata mai zaman kanta, to akwai bukatar kuyi bincike a kan wurin. Domin kuwa yana da kyau duk lokacin da aka kiraka ganawa, don daukan ka aiki yazamana kana da masaniya yadda yakamata, akan wannan ma’aikatar da kuma matsayin.
Kana ku sani cewar burin ku, ba kawai ganawar ba, amma samun aikin. Akwai bukatar muta ne, su san cewar a duk lokacin da mutun zai rubuta wasikar neman aiki, to ya rubuta ta yadda masu karantawa zasu fahimci wane matsayi yake nema kuma wane irin kwarewa zai kaima ma’aikatar.
A lokacin da aka fara ganawar, mutun ya kasance, ya amincewa kan shi, kana duk lokacin da aka tambaye shi abu. Ya dinga amsa tambayar kuma yana kallon masu tambayar shi daya bayan daya. Kana akwai bukatar mutun ya dinga magana cikin natsuwa, kamala, girmamawa, duk wadannan suna daga cikin abubuwan da ake dubawa a lokacin ganawa ta daukar ma’aikaci.