Shugaban kamfanin sada zumunta na Facebook, Mark Zuckerberg, ya ce za su tallafa wa billiyoyin mutane su samu damar shiga yanar gizo. Kamfanin na hadin gwiwa ne da wani kamfanin samar da yanar gizo na kasar Faransa mai suna “Eutelsat.”
Kokarinsu shi ne su samar da karin mutane masu amfani da yanar gizo a kasashen Afirka da ke kudu da Sahara. Yanzu haka dai sun kammala shirye-shiryensu, don fara wannan aikin a tsakiyar shekarar 2016.
Kamfanin na Facebook, zai dauki dawainiyar biyan kudin samar da yanar gizon ga mabukata, don hada su da duniya baki daya. Kamfanin Facebook din, ya sake cewar “Amfanin kudinmu shi ne mu taimaka ma kasashe masu tasowa wajen cin moriyar rayuwarsu.” Duk dai da cewar kasashen Afrika na daga cikin kasashe masu samun cigaba wajen amfani da wayar hannu. Akwai bukatar mutun biyu 2 cikin biyar 5 su kasance suna da wayar hannu kamin nan da shekarar 2020.