Accessibility links

Matasa a jihar Gombe, sun yi wata zanga zanga na nuna rashin jindadin su game da rashin nada kwamishinoni da wasu manyan mukamai a jihar

Matasa a jihar Gombe, sun yi wata zanga zanga na nuna rashin jindadin su game da rashin nada kwamishinoni da wasu manyan mukamai a jihar.

Matasan dai sun gudanar da zanga zangar ce dauke da kwalaye rubuce da sunayen mutanen da suke son a baiwa mukamai.

Wannan hali na matasan yasa Gwamna Dankwambo, cikin fushi ya gargadi matasan, ya kara da cewar duk wanda aka rubuta sunan sa akan kwali yana iya hana masa mukami koda ko sunan san a cikin wadanda ake son baiwa.

Wani dan jamiyyar PDP, a jihar Gombe, Malam Garba Inuwaa koma gona,yace jawabin Gwamnan bai yi masu dadi ba domin bayyana ra’ayi shine dimokradiya.

XS
SM
MD
LG