Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Firayim Ministan Pakistan ya lashi takobin daukan fansa


Nawaz Sharif Firayim Ministan Pakistan

Ranar Lahadi ne yayinda kiristoci ke bikin Easter aka kai munar bakin wake da ya yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da saba'in

Firayim ministan Pakistan Nawaz Sharif ya lashi takobin dakile ayyukan ta'adanci tare da daukan fansa kan wadanda suka da hannun a harin kunar bakin wake da aka kai kan kiristoci yayinda suke bikin Easter ranar Lahadi.

Harin ya lakume akalla mutane saba'in da biyu da suka hada da yara kimanin talatin kana wasu dari da uku suka jikata.

Wani mai magana da yawun rundunar sojojin kasar ya fada jiya Litinin cewa hukumomin tsaro sun kammala samame da dama bisa ga bayanan siri da suka samu. Sanadiya samamen sun kama wasu da ake zaton suna da hannu a harin.

Iyaye suna binne 'ya'yansu da suka mutu a harin kunar bakin wake da aka kai kan kiristoci
Iyaye suna binne 'ya'yansu da suka mutu a harin kunar bakin wake da aka kai kan kiristoci

XS
SM
MD
LG