Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsarin Karatu Irin Na Kasar Jamus Tsari Ne Mai Kyau In Ji Farfesa Hafiz Abubakar


Farfesa Hafiz Abubakar Mataimakin Gwamnan jihar Kano

Shirin samarwa matasa aikin na jihar Kano shine babbar hanyar bi

A kokarin ta na samarda aikin yi ga matasa Gwamnatin jihar Kano, ta kafa cibiyoyin koyan sana’oi kimani guda ashirin da hudu a jihar domin taimakawa matasa dogaro da kai.

Mataimakin Gwamnan jihar Kano, Farfesa Hafiz Abubakar, wanda ya bayyana haka ga muryar Amurka, yace baya ga kayan sana’oin Gwamnati na baiwa kowanen su jari domin ci gaba da sana’ar da ya koya.

Yace shirin yayi tasiri kwarai da gaske, kuma wannan a cewarsa shine babbar hanyar bi na samarwa matasa aikin yi.

Farfesa Abubakar, ya kara da cewa idan ana so a kouyawa mutane sana’a toh sai an dauki tsarin ilimi irin na Jamus, yana mai cewa tsarin irin na Jamus, basu damu da maganar digiri ba, tsarin karatun su na a tabbatar da cewa inda ka shiga makaranta ka fito ka iya wata sana’a, kowa zai dauke ka zai sameka kwararre ko zaka zauna da kanka kana da dama.

Mataimakin Gwamnan yace yanzu sau da dama Najeriya, kan yi hasaran kudade na wajen siyan kayan aiki, inda akan sayo su babu masu sarrafasu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:05 0:00

XS
SM
MD
LG