Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hillary Clinton Ta Lashe Zaben Zama 'Yar Takarar Democrat


Clinton ta samu kashi 78 cikin 100 yayin da Sanders ya samu kashi 21 cikin 100.

Jiya talata aka kammala kakar zaben fitar da dan takarar shugaban kasa na manyan jam’iuyyun Amurka inda Hillary Clinton ta doke Bernie Sanders a nan Washington, sannan kuma mutanen biyu suka yi ganawar da dukkansu suka ce mai amfani ce.

Clinton dai ita ce ake dauka a zaman wadda jam’iyyar Democrat zata tsayar a babban taronta na kasa da zata yi a wata mai zuwa a Philadelphia. Sanders ya ci gaba da kalubalantarta, duk da cewa tun watannin baya ta yi masa fintinkau. Hakan dai ya kara masa tasiri wajen shata irin manufofin da jam’iyyar zata yi takara kansu a zabe mai zuwa.

Sassan biyu sun bayarda sanarwa kusan iri daya inda suke cewa Clinton da Sanders sun Tattauna irin abubuwan da dukkansu suka dora wa muhimmanci, kamar yin karin albashi, sauya dokokin samar da kudaden yakin neman zabe tare da rage tsadar kudin karatun jami’a.

Har ila yau sun yi nuni da irin mummunar barazanar da suka ce Amurka tana fuskanta daga Donald trump.

A zaben fitar da dan takara na Washington, Clinton ta samu kashi 78 cikin 100 yayin da Sanders ya samu kashi 21 cikin 100. Wannan yaba Clinton adadin wakilai dubu 2 da 219 da ta lashe a zabe, shi kuma Sanders yana da dubu 1 da 832. Wannan adadi ya nuna Clinton kai tsaye ba ta lashe yawan wakilai dubu 2 da 383 da ake bukata domin zamowa ‘yar takara ba, amma kuma tana da goyon bayan manyan wakilai masu yawan da zasu iya ba ta nasara a lokacin babban taron.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG