Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kori Wasu Hafsoshin Soja A Nijar


Wannan wani bangare na ci gaban binciken Sojojin da ake zargi da yunkurin kifarda gwamnatin kasar ta Nijar

Wasu Sojojin kasar Nijar biyu sun rasa aikin su, wadannan Sojojin dai suna cikin wadanda ake zarki da yunkurin kifarda gwamnatin shugaba Issoufou Muhammadou, a watan Disambar da ta gabata.

A wata takarda da shugaban Issoufou Muhammadou, ya sakawa hannu aka sanan da wadannan hafsoshin Soja, Awwal Hambali da Ossoufou Oumarou, cewa an tube masu kakin sun a Soja, saboda samun su da aikata mummunar laifi.

Wannan wani bangare na ci gaban binciken Sojojin da ake zargi da yunkurin kifarda gwamnatin kasar ta Nijar a shekarar data gabata.

Babban sakataren gwamnati Gandou Zakara, da wakilin muryar Amurka, Souley Mumuni Barma, ya tuntuba yace masa yana wani taro.

Yanzu haka dai wanna mataki na korar Awwal Hambali, da Issoufou Oumarou, daga aikin Soja shine labarin da yafi daukar a jaridun kasar.

Sai da abun lura shine, takardan dake bayana matakin shugaba Issoufou Muhammadou, na tubewa Sojojin kaki bata dauke da sa hannun wadannan hafsoshi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG