Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Batun Canjin Yanayi Zai Sami Fifiko A Tattaunawar Canada


Tuni Amirka da Canada suka yi alkawarin rage yawan gas mai guba da masana’antu ke fitarwa

Matsalar canjin yanayi ne batun da shugaba Barack Obama na Amirka zai baiwa fifiko a tattaunawar da zai yi a kasar Canada yau Laraba a yayinda yake halarta taron kolin kasashen kudancin Amirka a birnin Ottawa.

Prime Ministan Canada Justin Trudeau da shugaban kasar Mexico Pena Nieto zasu bi sahun shugaba Obama wajen bada sanawar wani shirin hadin gwiwa da nufin samar da wutar lantarkin kasashen daga wasu kafofi kan shekara ta dubu biyu da ashirin da biyar.

Tuni Amirka da Canada suka yi alkawarin rage yawan gas mai guba da masana’antu ke fitarwa da wajen kashi arba’in zuwa kashi arba’in da biyar daga cikin dari, kasa da adadin da aka yarda za’a rage a shekara ta dubu biyu da goma sha biyu cikin shekaru goma masu zuwa.

Haka kuma batun harkokin cinnikayya tsakanin kasashen zai zama akan ajandar taron na yau Laraba. Kasashen

Mexico da Canada sune manyan kasashe guda biyu da suke harkar kasuwanci da Amirka, kuma a bara Canada itace kasar data fi kowace kasa sayen kayayyakin da aka sarafa anan Amirka.

Fadar shugaban Amirka tace, taron kolin zai bada sukunin jaddada muhimmancin kasashen kudancin Amirka.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG