Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka da Wasu Kasashen Turai Sun Kakabawa Wasu Jami'an Jamhuriyar Dimokradiyar Kwango Takunkumi


Shugaban Jamhuriyar Dimokradiyar Kwango Joseph Kabila da matarsa

Amurka da wasu kasashen Turai sun kargafawa wasu jami’an gwamnatin Junhuriyar Demokradiyar Congo takunkumin horo saboda rawar da suka taka wajen tada zaune-tsaye don a jinkirta gudanarda zabe a kasar.

Kamata yayi wa’adin mulki na biyu kuma na karshe na shugaba Joseph Kabila ya kare nan da mako guda, a ran 19 ga watan nan na Disamba, amma zai ci gaba da zamansa akan karaga a dalilin wata yarjejeiyar da akace an kulla da wani rukuni na ‘yan adawa, wanda zai bashi damar zama a kan kujerarsa ta mulki har zuwa shekarar 2018.

Sai dai mafi yawan jam’iyyun adawa duk sun ki yarda da wannan shirin, suna cewa sai shugaban ya sauka daga mulki a ranar Litinin mai zuwa.

Daga cikin wadanda aka dauki matakan horaswa a kansu din har da mataimakin frayim-ministan Congo din, Evariste Boshab da kuma Kalev Mutondo, shugaban Hukumar Leken Asiri ta kasar.

XS
SM
MD
LG