Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar 'Yansanda da Gwamnatin Jihar Ogun Sun Sha Alwashin Wadanda Suka Sace Wasu 'Yan Makaranta da Malamansu


Türkiyə ordusu sərhəd Akçakale şəhərində<br /> <br /> <br /> &nbsp;

Wasu da ba'a san ko su wanene ba sun sace daliban makarantar Nigeria-Turkish dake Isheri a jihar Ogun su biyu tare da malaman makarantar biyu lamarin da ya tada hankalin gwamnatin jihar da rundunar 'yansanda

Gwamnatin jihar Ogun tare da rundunar 'yansandan jihar sun yi alkawarin gano daliban biyu da malamansu biyu da aka sace a Isheri a karshen makon da ya gabata.

Gwamnan jihar Sanata Ibikunle Amosu yace yana baiwa jama'ar jihar tabbacin cewa nan ba da dadewa ba jami'an tsaro zasu gano wadanda suka sace mutanen.

Ya kira jama'a da su baiwa jami'an tsaro hadin kai domin a cimma nasara. Haka shi ma kwamishanan 'yansandan jihar Muhammad Iliyasu yace da yaddar Allah zasu zakulo wadanda suka sace daliban da malamansu.

Satar mutane a Najeriya na faruwa a sassa daban na kasar domin neman kudin fansa.

Ga rahoton Hassan Umaru Tambuwal da karin bayanai

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:41 0:00

XS
SM
MD
LG