Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Kasar Iraqi Ta Dauki Matakin Ladabtar Da Kurdawa A Kasar


Ayatollah Sadiq Hussaini Shirazi is an Iraqi Shi'a Marja, and the brother of the late Ayatollah Sayed Muhammad Shirazi.

Kuria'ar neman cin 'yancin gashin kai da Kurdawan kasar Iraqi suka jefa baiyi wa gwamnatin kasar dadi ba.Yanzu haka dai majilisar dokokin kasar ta umurci Prime Minister Haider Al-Abadi da ya dauki mataki kan jefa wannan kuri'ar da kurdawan suka yi.

A daidai lokacin da Kurdawa ke tsallen murnar nasarar da suka samu na kuri’ar da mutanensu suka jefa na amincewa da su kafa yankin kansu mai cin gashin kansa, hukumomin Iraq din su kuma sun tashi haikan wajen daukan matakan horad da Kurdawan kan wannan kuri’ar tasu.

Daya daga cikin matakan farko da gwamnatin Iraq ta dauka shine rufe sararin samaniyar yankin don hana wa duk wasu jiragen sama shiga wurin.

Haka kuma Iraq tace zata hade kai da kasar Turkiyya don gudanarda atisayen sojojinsu na hadin-gwiwa.

A jiya Laraba ne kuma Majalisar Dokokin Iraq, wacce tace kuri’ar da Kurdawan suka jefa ta sabawa Kundin tsarin mulki, suka umurci Pr.ministan Iraq, Haider al-Abadi, da ya aika rundunonin soja zuwa lardin Kurdawan na Kirkuk mai arzikin man fetur don su kwace dukkan rijiyoyin man fetur dake yankin.

Bayan duka wannan, Majalisar Dokokin ta Iraq ta nemi kasashe 34 dake da opishin jakadanci a can Kurdistan da cewa su rufe ma’aikatun, sannan kuma a sauke gwamnan jihar Najmaldin Karim daga kujerarsa ta mulki saboda wannan kuri’ar da ya bari aka jefa.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG