Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Jihar Nassarawa Tace Zataci Gaba Da Taimakawa 'Yan Gudun Hijira


Yan Gudun Hijira Dake Zaune A Cibiyar Jinya Ta Gulun Clinic Dake Jalingo

Gwamnatin jihar Nassarawa tace zata ci gaba da taimakawa 'yan gudun hijira, kuma gwamnan yace zai tabbatar sai an inganta matakan tsaro a yankin da suke

Yanzu haka dai dubban ‘yan gudun hijira daga jihar Benue ne suka kwarara zuwa garin Tunga dake cikin karamar hukumar Awe a jihar Nassarawa.

‘Yan gudun hijiran wadanda yawancin su ‘yan kabilar tiv ne da Fulani sukace sun guje wa muhallan su ne domin gudun kar rikicin ya rutsa dasu.

To sai dai wani abu mai daure kai, shine ardon ardodin jihar Nassarawa Ardo Lawan Dono, ya shaidawa wakiliyar sashen Hausa Zainab Babaji cewa, ba makiyaya ko manoman na jihar ta Benue ne suka kawo wannan fadan ba.Yace wannan yasa suke zaune lafiya da junan su.

Sai dai duk lokacin da irin haka ta faru wannan gari na Tunga yakan cika da jamaa domin yana zama tamkar tudun natsira ne.

Shugaban kungiyar raya al’ummar garin na Tunga Alhaji Saidu Mohammad ya bukaci gewamnati dama masu hannu da shuni da su taimaka musu domin ko kudin kungiyar ya kare wajen agajin da suke baiwa wadannan mutanen dake gudun hijira a garin nasu.

Gwamnan jihar ta Nassarawa yace sun kashe kudi har sama da naira miliya 50 domin agazawa wadannan bayin ALLAH kuma ba zasuyi kasa a gwiwa ba.Haka kuma zai tabbatar an inganta matakan tsaro a wannan yankin.

Ga Zainab Babaji da Karin bayani 3:32

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG