Matan Hausawa Sun Fara Shiga Wasannin Gymnastics
Ba kasafai ake samun mata Hausawa ke shiga wasannin motsa jiki ba, musamman wasannin Gymnastics wadanda ake amfani da lankwasa jiki da atisaye. Hakan kuwa saboda tasirin al'ada ce ta mutanen yankin. Sai dai wasu matan Hausawa a Abuja, sun shiga wannan wasa inda suke bukatar sauya wannan lamari.