Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 8 A Wajen Bikin Zagayowar Ranar Haihuwa a Afirka Ta Kudu


Yan Sanda a wurin da aka yi harbi a kasar Afirka ta Kudu
Yan Sanda a wurin da aka yi harbi a kasar Afirka ta Kudu

Wasu yan bindiga sun bude wuta kan gungun mutanen da suke murnar zagayowar ranar haihuwa a wani gari a kasar Afirka ta Kudu, inda suka kashe takwas tare da raunata wasu uku, kamar yadda ‘yan sanda suka bayyana a ranar Litinin.

Mutumin da ake tayawa bikin na cikin wadanda aka kashe a harin da aka kai a garin Gqeberha mai tashar jiragen ruwa da ke kudancin kasar, a da aka sani da Port Elizabeth.

“Maigidan gidan yana bikin murnar zagayowar ranar haihuwarsa ne, wasu ‘yan bindiga biyu da ba a san ko su wanene ba suka shiga tsakar gidan ranar Lahadi da yamma, kuma suka fara harbin kan mai uwa dawabi,” a cewar wata sanarwa da ‘yan sanda suka fitar.

‘Yan bindigar sun “harbe mahalarta bikin ne da gangan,” in ji ‘yan sandan, inda suka kara da cewa “mutane takwas ne suka mutu yayin da wasu uku ake ci gaba da fafatawa don ceto rayukansu a asibiti. Mai gidan na cikin wadanda suka mutu”.

Har yanzu dai ba a san dalilin kai harin ba.

Nomthetheleli Mene, babban jami'in 'yan sandan lardin na gabashin Cape, ya yi Allah-wadai da kashe-kashen da cewa "wani raini ne ga rayuwar bil'adama".

An fara gudanar da bincike kan harin, kuma ‘yan sanda sun ce ana farautar wadanda suka kai harin.

Rikici ya zama ruwan dare a Afirka ta Kudu, wadda ke cikin jerin kasashen dake samun yawan kashe-kashe a duniya, sakamakon tashin hankalin kungiyoyin daba da kuma barasa.

A shekarar da ta gabata ne aka kai hare-hare da dama a kasar Afrika ta Kudu, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane kusan dozin biyu, a wasu wuraren shan barasa daban-daban a unguwannin matsakaitan masu kudi, a birnin Johannesburg da kuma a gabashin birnin Pietermaritzburg.

Ministan 'yan sanda Bheki Cele, da kwamishinan 'yan sanda na kasa Fannie Masemola, da kuma kwararrun masu binciken aikata laifuka, an shirya za su ziyarci wurin da harin ya faru a safiyar ranar Litinin.

XS
SM
MD
LG