Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zagayowar Ranar Samun 'Yancin Amurka


Tutar Amurka
Tutar Amurka

Yanzu kuma ga shrhin muryar Amurka dake bayyana muku ra'ayin gwamnatin Amurka.

A yau Amurkawa ke bikin cika shekaru 247 da kafa Amurka. A ranar 4 ga watan Yuli, 1776, Majalisar wakilan yankunan Amurka wadda a lokacin ita ce ke gudanar da harkokin gwamnatocin yankuna 13 na nahiyar Amurka ta arewa, ta amince da bayanan karshe a kan sanarwar 'yancin kai. Ta hanyar wannan mataki, yankunan da suka zama jihohi 13 daga baya sun bayyana wa duniya samun 'yancinsu daga masarautar Burtaniyya.

Matakin yanke alaka da masarautar Burtaniyya ya dauki shekaru da dama, wanda ya bayyana yadda wadanda aka yi wa mulkin mallaka ke nuna takaici kan yadda ake gudanar da mulkinsu. Sun nuna rashin jin dadinsu kan yunkurin da gwamnatin Burtaniyya ta yi na daukar tsauraran matakai a kansu, da kuma sanya harajin da ya wuce kima don samun hanyar biyan basussuka masu dimbin yawa na masarautar Ingila.

Sanarwar samun 'yancin ita ce matakin koli a shekarun da aka kwashe ana yaki, don canza wadannan tsauraran matakan. An fara yakin juyin juya halin Amurka shekara daya kafin nan, a watan Afrilun 1775. Lokacin da aka gama shi a 1782 da kuma nasarar da wadanda aka yi wa mulkin mallaka suka samu, sabuwar kasar ta sami 'yanci don fidda nata tsarin, da bude masana'antu, da fitar da kayayyaki waje da kuma kasuwanci a kasashen waje. Tattalin arzikin ya bunkasa kuma a farkon wannan karni, Amurka ta fara samun suna a matsayin kasa mai bada dama, inda mutane za su iya fara sabon abu, samun dukiya ba tare da ganin kowa ba.

"A ko yaushe Amurka tana ci gaba, ta na kuma kara kokari. Wannan ita ce muhimmiyar kalma, muhimmin buri, jigo a cikin rayuwar al'ummar kasarmu: ci gaba, da samar da dama, cika alkawura. Wannan shi ne labarin Amurka, ”a cewar Shugaba Joe Biden.

"Amma a kowace rana, muna tuna cewa babu wani abin da ke da tabbas game da dimokuradiyyar mu, babu abin da ke da tabbas game da rayuwarmu. Dole ne mu yi gwagwarmayar don ita, mu kare ta, kuma mu same ta ta hanyar jefa kuri'a don samun daidaito, sake habbaka, da kuma fadada kiran Amurka na ci gaba gaba gadi ba tare da tsoro ba, "a cewar sa.

“Wannan rana tana tunatar da mu abin da ya hada mu tun da dadewa, abin da ya hada kanmu har yanzu, abin da muke wa kokari. "Mu mutanen kasar" ba wata magana ba a Amurka. "Mu mutanen" da ke yin duk abin da za mu iya yi don tabbatar da cewa burin Amurka da dalilin samun 'yanci da adalci da daidaito ya kaucewa rarrabuwa a zamaninmu, amma yana haskakawa kamar rana don haskaka makomar duniyarmu.”

XS
SM
MD
LG