Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Majalisar Dinkin Duniya Ta Ce Dole Isra'ila Ta Kaucewa Kisan Kiyashi A Gaza


Alkalan Kotun Kolin Majalisar Dinkin Duniya
Alkalan Kotun Kolin Majalisar Dinkin Duniya

Kotun kolin Majalisar Dinkin Duniya a ranar Juma'a ta ce dole ne Isra'ila ta kaucewa duk wani  aikata kisan kiyashi a Gaza tare da samar da agajin gaggawa da ake bukata a yankin da aka yi wa kawanya. 

Hukuncin Kotun Kolin ta MajalisarDinkin Duniya ta zartar ya ja hankalin duniya matuka.

Kotun ta bukaci Isra'ila da ta guji duk wani abu da ka iya yi na kisan kare dangi yayin da take matsa wa sojojinta a Zirin Gaza, duk da cewa Isra’ila ta kasa tsagaita wuta.

Dole ne Isra'ila ta dauki "matakai masu inganci da gaggawa don ba da damar samarda ayyukan yau da kullun da ake bukata da kuma taimakon jin kai don magance munanan yanayin rayuwa da Falasdinawa ke fuskanta," in ji kotun.

A wannan mataki, ICJ ba ta la'akari da ko Isra'ila na aikata kisan kiyashi a Gazabane – asali ma dai wannan tsari zai dauki shekaru da yawa.

Amma kotun ta gargadi Isra'ila da ta "dauka dukkan matakan da za ta iya don hana" ayyukan da za su iya fada karkashin yarjejeniyar kisan kare dangi ta Majalisar Dinkin Duniya, da aka kafa a shekara ta 1948 a lokacin da duniya ta barke daga mummunan kisan kiyashi na Nazi.

Ya kuma ce ya kamata Isra'ila ta "hana tare da hukunta" duk wani yunkuri na yin kisan kare dangi.

Afirka ta Kudu ce ta kawo karar, wacce ta zargi Isra'ila da keta yarjejeniyar kisan kare dangi ta Majalisar Dinkin Duniya.

Fiye da kwanaki biyu na sauraren karar a farkon wannan watan a dakin katafarendakin taro na fadar zaman lafiya, inda kotun ta ICJ ta zauna, lauyoyin bangarorinbiyu sun fafata da ita kan fassarar wannan Yarjejeniyar.

Afirka ta Kudu ta zargi Isra'ila da ayyukan "kisan kare dangi" wanda Afrika yaKudu ke zargin haifar da "lalata wani bangare na Falasdinawa da kabilanci."

Ta bukaci kotun da ta umurci Isra'ila da ta "dakatar da" ayyukan soji a Gaza tare da barin agajin jin kai ya isa ga fararen hula a can.

Isra'ila ta yi watsi da lamarin a matsayin "gurbataccen labari" kuma ta ce babbanaikata aikin kisan kare dangi shi ne harin ta’addancin da Hamas ta kai wa Isra’ilana ranar 7 ga Oktoba.

Babban lauyan Isra'ila Tal Becker ya ce "Abin da Isra'ila ke nema ta hanyar yin aiki a Gaza ba shine ta lalata al'umma ba, amma don kare jama'a, mutanenta, wadanda ke fuskantar hare-hare ta bangarori da yawa."

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG